A cewar rahoton sashen ƙasa da ƙasa na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza da ya samo daga shafin Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), a ranar Litinin (29 ga watan Zul-Hijjah, shekara ta 1447H), ya gabatar da jawabin rufe "Mu'utamar na Kwamitin Ashura da Tattakin Arba'een" a gidansa da ke Abuja, inda ya yi bayani kan matsayin juyin juya halin Imam Husaini (AS) da kuma tsoron da makiya suke da shi game da wannan harka.
Muhimman Sassan Jawabin Sheikh Zakzaky:
Asalin Tarihi na Ashura da Arba'een:
Ya yi nuni da cewa lamarin Ashura da Tattakin Arba'een ba sabbin abubuwa ba ne, yana mai jaddada cewa wannan yunkuri yana da tushe da asali mai zurfi a Musulunci; ta yadda tun kafin faruwar wannan waƙi'ar, an riga an bai wa Manzon Rahama (S) labarinta, kuma sanannen al'amari ne a tarihi.
Tsoron Makiya Ga Farkawar Al'umar Musulmi:
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya bayyana cewa maƙiya suna tsananin tsoron tasiri, yaɗuwa, da karɓuwar al'adun Ashura a tsakanin mutane, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa suke yin yunkurori daban-daban don ganin sun dakatar da wannan tafiya.
Tsayuwa Tsayin Daka Agaban Barazana:
Cikin daddadan sauti da nuna jaruntaka, Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa: "Duk wata barazana ba za ta sa mu daina abin da muke yi ba." Ya kara da cewa abin da maƙiya suke tsoro shi ne zuwan lokacin wayewar kai, fahimtar gaskiyar Ahlul Baiti (AS), da kuma samun karfi da yawaitar mabiya bayan dogon lokaci na rauni da ƙarancin mabiya.
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran A Matsayin Misali Na Juriya:
A ƙarshe, ya yaba da tsayin dakan da kasar Iran ta nuna, inda ya jaddada cewa nasara da ɗaukakar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da ita a yau, sakamakon tsayuwar daka ne a kan wannan tafarki. Ya tabbatar da cewa wannan ita ce hanyar yaki da zalunci da tabbatar da adalci.









Ra'ayinka